1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Jagoran adawa a Somaliland ya lashe zaben shugaban yankin

November 19, 2024

Jagoran adawa a Somaliland Abdirahman Mohamed Abdullahi wanda aka fi sani da Irro ya kada shugaban yankin mai ci Muse Bihi Abdi a zaben da aka gudanar duk dai a kokarin yankin na samun amincewar duniya a matsayin kasa.

https://p.dw.com/p/4n9wf
Shugaban Somaliland Muse Bihi Abdi a birnin Addis Ababa na kasar Habasha
Shugaban Somaliland Muse Bihi Abdi a birnin Addis Ababa na kasar HabashaHoto: TIKSA NEGERI/REUTERS

Somaliland dai na cin gashin kanta tun bayan ballewa daga kasar Somaliya a 1991, duk da cewa hukumomin kasa da kasa basu amince da ita ba a matsayin kasa mai cikakken iko wanda hakan ya sanya hukumomin kakaba mata takunkumin karayar tattalin arziki da kuma hana manyan jami'an gwamnatin yankin zirga-zirga a kasashen ketare.

Karin bayani: An gudanar da zaben shugaban kasa a Somaliland

Hukumar zaben kasar ta ce jagoran adawar Mr. Irro na jam'iyyar Waddani ya lashe zaben da kaso 64% bisa 100, yayin da shugaba mai ci Bihi ya samu kashi 35% bisa 100 na yawan kuri'un da aka kada. 

Ana sa ran rantsar da sabon shugaban a ranar 14 ga watan Disambar 2024. Irro ya taba zama jakadan Somaliya a tsohuwar Tarayyar Soviet da kuma Finland, kazalika ya kuma taba zama kakakin majalisar dokokin Somaliya mafi dadewa kafin ballewa daga kasar.