1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: Karfafa huldar tsaro da Italiya

Gazali Abdou Tasawa LMJ
October 19, 2022

Kasashen Nijar da Italiya sun karfafa huldarsu a fannin tsaro da yaki da ta'addanci, yayin wata ziyara da tawagar manyan jami'an gwamnati da na rundunar sojojin Italiya suka kai a Nijar din.

https://p.dw.com/p/4IQc2
Nijar | Diffa | 'Yan Gudun Hijira
Matsalar tsaro dai, ta tarwatsa mutane da dama a yankin SahelHoto: Gazali Abdou Tasawa/DW

Yayin wannan ziyara dai, kasashen na Nijar da Italiya sun yi bitar huldar tsaro da ta hada kasashen biyu shekaru biyar bayan kaddamar da ita a shekara ta 2017. Haka kuma tawagar jami'an gwamnatin Italiyan karkashin jagorancin ministan tsaron kasar Lorenzo Guerini da kuma shugaban hafsan sojojin kasar, ta sanar da shirin taimakon Nijar din da karin wasu jiragen yaki biyu masu saukar ungulu da za ta aike da su a shekara mai zuwa. Bayan ganawa da shugaban kasa Mohamed Bazoum a fadarsa, tawagar ta gudanar da taro da ministan tsaron kasar ta Nijar Alkassoum Indatou da kuma shugabannin sojojin Jamhuriyar ta Nijar. Ministan tsaron kasar ta Italiya Lorenzo Guerini ya bayyana Nijar din a matsayin kasa mai matukar muhimmanci ga zaman lafiyar yankin Sahel da yaki da ta'addanci da ma fataucin dan Adam a duniya, a dangane da haka ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen kawo mata goyon baya a kokowar da take ta tsaron lafiyar al'ummarta da kuma taka birki da kungiyoyin 'yan ta'adda.

Burkina Faso | hari | Sojoji | Sintiri | Faransa
Faransa na cikin kasashen da ke bayar da tallafin soja a ynakin SahelHoto: Michel Cattani/AFP

A nasa bangaren ministan tsaron Jamhuriyar ta Nijar Alkassoum Indatou yabawa ya yi da irin kokarin da Italiyan ke yi, wajen bayar da horo ga sojojin kasarsa da kuma yadda huldar harkokin tsaron da ta hada kasashen biyu ke tafiya cikin mutunta juna. Bitar huldar harkokin tsaron da ta hada kasashen Nijar da Italiyan ta wannan loakci, na zuwa ne a daidai lokacin da aka fara samun ingantuwar tsaro a kan iyakokin kasar da dama. To amma kuma hukumar 'yan sanda ta Nijar din ta nuna damuwa kan yadda yanayin tsaro ke tabarbarewa a cikin birane musamman a birnin Yamai, inda ake samun karuwar sace-sacen da kwacen babura da na salula ta hanyar amfani da wasu babura marasa takardu da lamba. Akan haka ne hukumar 'yan sandan ta yi kira ga masu babura da su gaggauta yi mus lamba da sauran takardu, domin taimakawa wajen shawo kan wannan matsala.