Isra'ila zata hukunta sojojin da suka aika laifuka a Gaza
July 6, 2010Hukumomin Sojan Isra'ila sun ce za su ɗauki matakin ladabtarwa a kan wani sojan ta da ake zargi da kisan wasu mata Palasɗinawa biyu, a lokacin yaƙin Gaza duk kuwa da nuna farar tuta na saranda da suka yi.
A wata sanarwa da hokumomin sojan na Israila suka fitar a yau, sun ce an hukunta wani kwamandan bataliyan soja wanda ya bar sojojin sa suka yi garkuwa da wasu Palasɗinawa da kuma wani sojan na daban da ake zargi da ba da umarnin kai hari a kusa da wani masallaci dake yankin na Gaza.
A ƙarshen shekarar 2008 ne dai Isra'ila ta ƙaddamar da wani hari a kan yankin Gaza wanda ya haifar da mutuwar mutane 1400, akasarin su fararen hula, abinda kuma ya jawo wa Isra'ilan suka daga ƙasashen duniya daban-daban.
Mawallafi: Babangida Jibril
Edita:Ahmad Tijani Lawal