1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Isra'ila za ta maida martani kan hari daga Labanan

July 29, 2024

Isra'ala ta sha alwashin mayar da martani a kan harin da aka dora alhaki a kan kungiyar Hezbollah a Tuddan na Golan a ranar Asabar, wanda ya kuma kashe wasu yara da matasa 12.

https://p.dw.com/p/4iqjj
Ministan tsaron Isra'ila, Yoav Gallant lokacin ziyara a yankin Tuddan Golan
Ministan tsaron Isra'ila, Yoav Gallant lokacin ziyara a yankin Tuddan GolanHoto: Menahem Kahana/AFP/Getty Images

Majalisar tsaro a Isra'ila ta amince wa Firaminista Benjamin Netanyahu, da ya dauki mataki a kan harin rokoki da aka kai a yankin Tuddan Golan.

A jiya Lahadi ne dai Mr. Netanyahu ya kira taron majalisar tsaron kasar, bayan komawarsa kasar daga kasar Amurka da ya kai wa ziyara a makon jiya.

Isra'alar dai ta sha alwashin mayar da martani a kan harin da aka dora alhaki kai shi a kan kungiyar Hezbollah a Tuddan na Golan a ranar Asabar, wanda ya kuma kashe wasu yara da matasa 12.

A jiya Lahadi ma dai wasu hare-hare da dakarun Isra'ilar suka kaddamar da safiya sun fada cikin kasar Labanan.

Kungiyar Hezbollah da ke samun goyon bayan Iran, a wasu kasashe ke dauka ta ta'adda ce, ta nesanta kanta da harin.