1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Isra'ila za ta kare matsayarta a kotun duniya

May 17, 2024

A yau Juma'a 17 ga watan Mayun 2024, Isra'ila za ta kare matsayarta a kotun kasa da kasa da ke birnin Haque, kan bukatar Afrika ta Kudu na neman takawa Benjamin Natenyahu, aikata kisan kare dangi a Rafah da ke Gaza.

https://p.dw.com/p/4fxkz
Wasu masu zanga-zangar goyon bayan Falasdinu a harabar kotun ICJ da ke Haque a watan Janairu, 2024
Wasu masu zanga-zangar goyon bayan Falasdinu a harabar kotun ICJ da ke Haque a watan Janairu, 2024Hoto: Remko de Waal/ANP/AFP/Getty Images

Afrika ta Kudu ta bukaci kotun duniya da ta gaggauta dakatar da Isra'ila daga farmakin da take kai wa fararen hula a Rafah, duk da a gefe guda Isra'ilan ta ce ta kaddamar da farmakin ne da zummar murkushe mayakan Hamas. Hukumomin Tel Aviv sun sha kare matsayarsu na yakin Gaza tare da watsi da zargin Afrika ta Kudu inda suka ce zargi ne mara tushe.

Karin bayani: Isra'ila: Kotun kasa da kasa za ta yanke hukunci

Duk da bukatar babbar kawar Isra'ilan wato Amurka na dakatar da kai hare-hare kan birnin Rafah saboda dalilai na jinkai da kuma dubban Falsdinawan da ke zaune a yankin, Firaiministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya kafe kan ci gaba da kai farmakin duk da hadarin da hakan ka iya jefa fararen hula.

Karin bayani: Israila ta yi watsi da zargin kisan kare dangi a Gaza 

Hukumomin Pretoria sun gabatar da daftarin bukatu guda uku a gaban kotun na ICJ da suka hadar da bukatar gaggauta dakatar da Isra'ila daga kai hare-hare a Rafah da janyewar sojojin Isra'ilan daga yankin Gaza baki daya sai kuma bukatar shigar da kayan agajin jinkai a yankin.