1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Isra'ila ta zargi Hezbollah da kaiwa MDD hari a Lebanon

November 19, 2024

Ofishin Majalisar Dinkin Duniya da ke gudanar da ayyukan wucin-gadi a Lebanon ya ce wani harin da aka kai ofishin hukumar ya raunata ma'aikatanta guda hudu.

https://p.dw.com/p/4nAsD
Motocin kwantar da tarzoma na MDD dake aiki a Lebanon
Motocin kwantar da tarzoma na MDD dake aiki a LebanonHoto: Carl Court/Getty Images

Majalisar Dinkin Duniya ta ce ma'aikatanta guda hudu 'yan asalin kasar Ghana sun samu raunuka a yayin da aka harba masu makaman roka.

Karin bayani:Isra'ila ta kai sabbin hare hare a Beirut

Ministan Tsaron Italiya Guido Crosetto ya tabbatar da afkuwar lamarin inda ya ce mayakan Hezbollah ne suka kaddamar da harin wanda tun da fari ya dora alhakin kai harin kan dakarun sojin Isra'ila. Ofishin na Majalisar Dinkin Duniya UNIFIL ta ce ana yawan kai mata farmaki tun bayan kaddamar da hare-haren da Isra'ila ta kaddamar kan Hezbollah a Lebanon.