Isra'ila ta yi takaicin harbo jirgin Rasha
September 18, 2018Rundunar sojin Israila ta baiyana takaici da rasuwar jami'an sojin Rasha da ta ce an harbo jirginsu a bisa kuskure yayin wani farmaki, tana mai zargin shugaban Siriya Bashar al Assad da kuma Iran da haddasa faruwar hakan.
Israilar ta baiyana takaicin ne a wata sanarwa da rundunar sojin ta fitar a martaninta na farko bayan aukuwar lamarin.
Tun da farko a yau Talata Ministan tsaron Rasha Sergei Shoigu ya shaidawa Israila cewa ita ce ke da alhakin harbo jirgin a sararin samaniyar Siriya. Dukkan mutane 15 da ke cikin jirgin sun rasu.
Ministan tsaron na Rasha tattauna ta wayar tarho da takwaransa na Israila Avigdor Lierberman inda ya baiyana masa rashin jin dadinsu.
Rundunar sojin Rasha ta ce Israila ba ta yi wani gargadi ko sanar da ita cewa za ta kai hari yankin Latakia ba kafin ta kai farmakin.