1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Isra'ila ta ayyana kashe jagoran Hezbollah Nasrallah

September 28, 2024

Isra'ila ta sanar da halaka jagoran Hezbollah da ke samun goyon bayan Iran Hassan Nasrallah tare da wasu kwamandojin kungiyar a kudancin Beirut, duk da cewa Hezbollah ba ta fitar da sanarwa a hukumance ba.

https://p.dw.com/p/4lBq7
Jagoran Hezbollah Hassan Nasrallah
Jagoran Hezbollah Hassan NasrallahHoto: Al Manar TV/AP/picture alliance

Dakarun sojin Isra'ila na ci gaba da luguden wuta a kudancin Beirut domin murkushe burbushin mambobin kungiyar ta Hezbollah, duk da nasarar kashe jagoran kungiyar Hassan Nasrallah, a cewar mai magana da yawun sojojin Isra'ilan Laftanal Kanan Nadav Shoshani a yayin da yake tabbatar da mutuwar Nasrallah a shafinsa na X.

Karin bayani:'Isra'ila za ta ci gaba da yakar Hezbollah' 

Da yake gabatar da jawabi a zauren Majalisar Dinkin Duniya awanni gabanin kai farmakin, Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya sha alwashin ci gaba da gwabza yaki da Hezbollah da Hamas har sai ya ga bayansu.

HALIN DA AKE CIKI A BEIRUT

Hayaki dai ya turnuku sararin samaniyar Beirut, tituna sun kasance fayau, kantuna a rufe ba ka jin motsin mutane. Wata majiyar kamfanin dillancin labarai na Reuters ta shaida jin karar tashin makamai masu linzami sama da 20 ta sararin samaniya. Dubban mutane sun kauracewa gidajensu a yankin na kudancin Beirut, inda suka nemi mafaka a gabar teku da dandanlin shahidai da kuma wasu wuraren na daban da ke kasancewa tudun muntsira.

Karin bayani:Isra'ila ta kashe wani babban kwamandan Hezbollah a Beirut 

Isra'ila ta ce ta yi nasarar kakkabe wasu daga cikin rokokin da Hezbollah ta harba cikin kasarta akalla guda 10, duk da cewa ba ta yi cikakken bayani ba kan nau'ikan makaman na Hezbollah. Hukumomin Lebenon sun ce tuni aka fara kwashe dukkan marasa lafiyan da ke asibitocin kudancin Beirut, yankin da Isra'ila ke ci gaba da ruwan bama-bamai ta sama.

Jagoran Hezbollah Hassan Nasrallah a tsakiya a wajen wani taro a 2006.
Jagoran Hezbollah Hassan Nasrallah a tsakiya a wajen wani taro a 2006.Hoto: Dohrn Michael/ABACA/picture alliance

Sama da mutane 750 ne suka mutu yayin da wasu dubban suka jikkata, tun bayan kaddamar da hare-haren da dakarun Isra'ilan kan mayakan Hezbollah.