1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaIsra'ila

Isra'ila ta kai hari bisa kuskure a Masar

October 22, 2023

Kasar Isra'ila ta ce dakarunta sun kai hari kan iyakar kasar Masar bisa kuskure, a kokarinsu na cimma mayakan Hamas da ke Zirin Gaza.

https://p.dw.com/p/4Xsfo
Wasu daga cikin dakarun Isra'ila a bakin dagaHoto: Mostafa Alkharouf/AA/picture alliance

Wata sanarwa da rundunar sojin Isra'ila ta fitar, ta nuna damuwa kan harind a ta kai bisa kuskure wanda ya jikkata wani jami'in bincike na kasar Masar. Hukumomin kasar Isra'ila sun sha alawahin kaddamar da bincike kan abinda ta kira harin kuskure.

Tuni dai mai magana da yawun rundunar sojin Masar Mahmoud Gamal ya fitar da sanarwar cewa wasu jami'an tsaron su sun samu raunuka a dalilin harin da Isra'ila din ta kai kasar.

Wannan harin dai na zuwa ne kwanaki kadan bayan da Isra'ilar ta bai wa 'yan kasarta da ke Masar umarnin ficewa daga kasar, bayan cimma yarjejeniyar fara shigar da kayan agaji ta iyakar Rafah zuwa zirin Gaza. Yanzu haka dai an fara dasa ayar tambaya kan makomar kayan agaji da ke shigowa ta iyakar Masar.