1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Iran ta kaddamar da hari a Isra'ila

Lateefa Mustapha Ja'afar
October 1, 2024

Rundunar sojojin Isra'ila ta bayyana cewa Iran ta kaddamar da harin makamai masu linzami, tare da bai wa al'umma umarnin su garzaya zuwa wuraren fakewa na ko-ta-kwana da ke kusa.

https://p.dw.com/p/4lJE4
Isra'la | Iran | Hari | Makamai | Fargaba | Rikici | Gabas ta Tsakiya
Makamai masu linzami da Iran ta harba Isra'ilaHoto: JACK GUEZ/AFP

An ji karar fashewar abubuwa yayin da tagogi suka girgiza a Tel Aviv da kuma kusa da birnin Kudus, koda yake babu tabbacin ko makaman da Iran din ta harba ne suka fashe a wuraren ko kuma sojojin Isra'ila sun yi nasarar dakile tasirinsu. Isra'ilan da Amurka sun yi gargadin cewa za su dauki mummunan mataki, in har Iran ta kai farmakin da ke nuna goyon bayan kungiyar Hezbollah ta Lebanon. Babu dai tabbacin irin barnar da makaman da Iran din ta harba suka yi, sai dai ana hasashen hakan ka iya fadada rikicin da a yanzu haka yake karuwa sannu a hankali a yankin Gabas ta Tsakiyar.