1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Isra'ila ta ce ba za ta halarci taron Masar ba

Zainab MohammedAugust 2, 2014

Isra'ila ta ce ba za ta shiga tattaunawar neman sulhu ba da Masar ta shirya domin samun masalha tsakaninsu da Hamas, saboda garkuwa da Hamas ke yi da wani sojinta.

https://p.dw.com/p/1Cnql
Gaza Israel Krieg Angriff 1. August
Hoto: Reuters

Sakataran harkokin wajen Amirka John Kerry ya zargi Hamas da kasancewar sanadiyyar wargajewar yarjejeniyar tsagaita buɗe wutar da aka cimma ta sao'i 72. A cikin wata sanarwa da ya bayyana Kerry ya buƙaci Hamas da ta sako wani sojin Isra'ila da aka rawaito cewar ya ɓace wanda kuma Hamas ke yin garkuwa da shi.

Sakataran harkokin wajen na Amirka ya kuma yi kira ga ƙasashen duniya da su matsa ƙaimi wajen ganin cewar sun dakatar da hare-haren rokoki ta hanyoyin ƙarƙashin ƙasa da Hamas ke kai ma Isra'ila. Shi ma babban sakataran Majalisar Ɗinkin Duniya Ban Ki Moon ya ce ya zama wajibi Hamas ta gaggauta sako sojin ba tare da gindaya wasu sharuɗa ba.Ƙungiyar Hamas dai ta musunta zargin cewar ta sace sojin na Isra'ila. Yazuwa yanzu Falasɗinawa 107 a kashe a hare-haren da dakarun Isra'ila suka kai a kudancin Gaza.

Mawallafi : Zainab Mohammed Abubakar
Edita : Abdourahamane Hassane