1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Isra'ila ta amince da tattaunawar tsagaita wuta a yakin Gaza

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
February 25, 2024

Mashawarcin firaministan Isra'ila Benjamin Naetanyahu kan harkokin tsaro Tzachi Hanegbi ya ce an fara tattaunawar a birnin Paris na Faransa kafin samun wannan ci gaba, kuma alamu sun nuna cewa ana dab da cimma masalaha

https://p.dw.com/p/4cqfY
Hoto: Florian Görner/DW

Isra'ila ta amince da sake aikewa da wakilanta zuwa Qatar domin ci gaba da tattaunawar sulhun cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a yakin Gaza, tare da musayar fursunoninta da ke hannun Hamas, kamar yadda wata kafar yada labaran kasar ta sanar.

Karin bayani:Isra'ila za ta tafiyar da tsaron ynakin Zirin gaza

Kamfanin dillancin labaran Faransa AFP ya rawaito mashawarcin firaministan Isra'ila Benjamin Naetanyahu kan harkokin tsaro Tzachi Hanegbi na cewa an fara tattaunawar a birnin Paris na Faransa kafin samun wannan ci gaba, kuma alamu sun nuna cewa ana dab da cimma masalaha.

Karin bayani:Jagoran Hamas Ismail Haniyeh ya isa Masar kan rikicin Gaza

Wakilin AFP ya ce a jiya Asabar kadai dakarun Isra'ila sun kai hare-hare har sau shida a Rafah.