1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Siriya: Isra'ila na ci gaba da mamaye Golan

Lateefa Mustapha Ja'afar
February 14, 2025

Rahotanni da ke fitowa daga Siriya na nuni da cewa, sannu a hankali Isra'ila na ci gaba da kutsawa tare da mamaye kauyukan kasar da ke kusa da Tuddan Golan.

https://p.dw.com/p/4qUs9
Siriya | Tuddan Golan | Isra'ila | Mamaya | Sojoji
Sojojin Isra'ila na ci gaba da mamaye kauyukan Siriya Hoto: Pavel Nemecek/CTK/picture alliance

Kungiyar Kare Hakkin dan Adam da ke sanya idanu a yakin Siriya ce ta sanar da hakan, inda ta ce ta samu rahoton an hango sojojin Isra'ila a birnin Al-Rafid kwanaki biyu bayan wasu rahotanni sun ce an hango sojojin Isra'ilan sun shiga birnin Kudana. Kungiyar ta ce an hango motocin sojojin Isra'ilan ma har guda 12 a birnin Saidna al-Golan, inda sojojin suka kafa wajen binciken ababen hawa. Sai dai rundunar sojojin Isra'ilan ta ce, ba za ta ce komai a kai ba.