1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Dakatar da kai hari ta kasa a Zirin Gaza

Lateefa Mustapha Ja'afar
October 25, 2023

Jami'an gwamnati Isra'ila da na Amurkan sun tabbatar da cewa, Isra'ilan ta amince ta dakatar da shirinta na kaddamar da hare-hare ta kasa nan take a yankiin Zirin Gaza na Falasdinu.

https://p.dw.com/p/4Y25n
Isra'ila |  Zirin Gaza | Hare-Hare | Hamas
Isra'ilan dai na ci gaba da kai hare-hare ta sama a yankin na Zirin GazaHoto: Ariel Schalit/AP Photo/picture alliance

Fitacciyar mujallar nan ta Amurka wato Wall Street da ta ruwaito labarin ta bayyana cewa, Isra'ilan ta dauki wannan matakin ne, domin bai wa Washington damar shigar da makaman kariya daga makamai masu linzami ga sojojinta da ke yankin. Rahoton mujallar ya ce, Isra'ilan na tunanin ta bayar da damar kai kayan agajin jin-kai ga fararan hular da yaki ya rutsa da su a Zirin na Gaza. Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito cewa, Amurka ta shawarci Tel Aviv ta dakatar da kaddamar da hare-haren ta kasa a yankin. A wani labarin kuma, firaministan Sweden Tobias Lennart Billström ya bayyana cewa mafita daya tilo ta kawo karshen rikicin Isra'ila da Falasdinu ita ce samar da kasashe biyu a yankin. Billström ya nunar da hakan ne, yayin wata hira da ya yi da tashar DW.