1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Siriya: IS ta kashe sojojin Amirka

Abdul-raheem Hassan
January 17, 2019

Harin kunar bakin wake ya yi sanadin mutuwar dakarun Amirka hudu a garin Manbij da ke arewacin Siriya, harin ya faru ne yayin da sojojin ke ganawa a wani gidan cin abinci.

https://p.dw.com/p/3BgVk
Syrien US-Militär in Manbidsch
Hoto: Getty Images/AFP/D. Souleiman

Ma'aikatar tsaron Amirka ta Pentagon ta tabbatar da mutuwar dakarun Amirka da ke aikin sintiri, amma ta ce za ta yi karin bayani da zarar ta kammala bincike kan harin. Kungiyar Syrian Observatory for Human Rights da ke rajin kare hakkin dan Adam mai mazauni a Birtaniya, ta ce harin ya kashe wasu mutane 16 tare da jikkata wasu da dama.

Harin na zuwa ne kasa da wata guda da bayan ikirarin shugaban Amirka Donald Trump na janye dakarun kasarsa daga Siriya. Tuni kungiyar IS ta dau alhakin kai harin kunar baken waken kan sojojin Amirka.