1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

IS ta dauki alhakin kai harin Burkina Faso

Abdoulaye Mamane Amadou
December 27, 2019

Kungiyar IS ta bayyana daukar alhakin kai harin a wani barikin sojan da ke arewacin Burkina Faso a ranar Talatar da ta gabata tare da halaka sojojin kasar da dama.

https://p.dw.com/p/3VPCo
Burkina Faso Anschlag ARCHIV
Hoto: picture-alliance/dpa/A. Yempapou

Kungiyar IS ta bayyana cikin wata sanarwa a wannan Jumma'a cewa reshenta da ke yammacin Afirka na (ISWAP) ne ya kaddamar da harin inda ya tayar da bam a cikin barikin sojan na Burkina Faso da ke Arbinda a lardin Soum da ke arewacin kasar tare da halaka sojoji da dama baya ga jikkata wasu

Burkina Faso na daya daga cikin kasashen yankin Sahel da 'yan ta'adda suka zafafa kai hare-hare musamman ma a barikin sojoji.