1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

IS ta dauki alhakin harin Manchester

Mouhamadou Awal Balarabe
May 23, 2017

Kungiyar IS ta ce ita ta kai harin Manchester da ya salwantar da rayukansu mutane 22. Tuni Sarauniyar Ingila Elisabeth ta mika sakon jaje ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu a harin

https://p.dw.com/p/2dRoH
UK Terror gegen Teenager: 22 Tote bei Anschlag auf Konzert in Manchester
Hoto: picture alliance/empics/D. Lawson

Kungiyar IS ta dauki alhakin harin ta'addancin da aka kai cibiyar raye-raye na birnin Manchester da ke yammacin Ingila, inda mutane 22 suka mutu yayin da 59 kuma suka jikata. Cikin wata sanarwa da ta watsa da kafofin sadarwa na zamani IS ta yi barazanar dasa wasu nakiyoyin.

Rundunar 'yan sandan Birtaniya ta ce wanda ya kai harin ya rasa ransa bayan da ya tada bam da ke daure a jikinsa. Sannan kuma ta bayyana cewar ta kama wani matashi mai shekaru 23 da haihuwa bisa zarginsa da marar hannu a wannan harin, wanda ya zo watanni biyu bayan na London da ya salwantar da rayukansu mutane biyar.

sarauniya Elisabeth ta Ingila ta mika jajenta ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu a harin na Manchester. Yayin da Firaminista Theresa May ta yi tir da wannan harin.