1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iran: Za mu dauki fansa kan Saudiyya

Abdul-raheem Hassan
February 21, 2019

Babban kwamanda da ke lura da rumbun makaman kasar Iran ya yi barazanar daukar fansa kan Saudiyya bayan wani mummunan hari da ya kashe dakarun juyin juya halin kasar 27 a Kudu maso gabashin kasar.

https://p.dw.com/p/3DopJ
Iran Rohani Hauhaltsrede im Parlament
Hoto: Getty Images/AFP/A. Kenare

Qasem Soleimani ya ce Saudiyya na amfani karfin kudi wajen cimma manufofinta a kasashen waje, Iran ta sha alwashin ramuwar gayya kan Saudiyya ta kowace hanya.

Kasar Iran na zargin Saudiyya da hadaddiyar daular Larabawa da mara baya ga 'yan tawayen da suka kaddamar da hari kan jami'an tsraonta, zargin da Saudiyya da makociyarta suka musanta.