Iran tace ba za ta bayar da kai ba...
November 20, 2013Shugaban addinin Iran Ayatollah Ali Khamenei ya fito fili ya bayyana cewa kasarsa ba ta da niyar dakatar da shirinta na nukiliya , sa'o'i kalilan kafin a koma kan teburin tattauna wannan batu a birnin Jeniva. Cikin wani jawabi da ya yi a gaban 'yan agaji dubu 50 da suka hallara a wani masallacin birnin Teheran, Khamenei ya jadadda 'yancin da kasarsa ke da shi na gudanar da shirin nukiliya na zaman lafiya.
Da ma tun da farko shugaba Barack Obama na Amirka ya ce kasarsa ba za ta yi gaggawar janye takunkumin karya tattalin arziki da ta kakaba wa Iran ba, sai idan ya ga yadda tattaunawa tsakaninta da kuma kasashen nan shida masu fada a ji a duniya ta kaya. Sannan kuma ya yi barazanar daukan matakin da ya dace idan taron na Jeniva ya wace ba tare da cimma matsaya ba.
A baya dai Iran da kuma kasashen nan biyar da ke da kujerar dindindin a kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da kuma Jamus, sun cimma yarjejeniyar wucin gadi wacce ta tanadi dakatar da gina cibiyar nukiliya ta Arak da kuma dakatar da aikin inganta makamashin Uranium da Iran ta sa a gaba.
Mawallafi: Mouhamadou Awal Balarabe
Edita: Umaru Aliyu