1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iran ta zartar da hukunci kan masu bore

November 16, 2022

Iran ta yanke hukuncin kisa ga mutane uku da ta kama yayin zanga-zangar kin jinin gwamnati a kasar, bisa laifukan ta'addanci.

https://p.dw.com/p/4Jctn
Iran, Teheran | Anhaltende Protest
Hoto: Merha

Kafar yada labaran kasar ta ruwaito cewa, an yanke wa masu boren kin jinin gwamnatin hukuncin ne bisa laifukan kashe jami'in dan sanda da kuma yada ta'addanci.

Sai dai dukkanin ukun na da damar daukaka kara.Hukuncin da aka yanke na wannan Larabar na zuwa ne kwanaki uku bayan da gwamnatin Iran din ta yanke makamancin wannan hukuncin ga wani da ta zarga da kona ginin gwamnati.

An gudanar da jerin zanga-zanga a kasar ta Iran sakamakon mutuwar matashiyar nan Mahsa Amini a hannun 'yan sandan gyara halinka a cikin watan Satumbar da ya gabata.