1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iran ta toshe shafin Google a ƙasar

September 24, 2012

Gwamnatin Iran ta toshe shafin internet ɗin nan na Google don nuna fushinta da fim ɗin batancin nan da aka yi wanda aka sanya shi a shafin YouTube mai alaƙa da Google.

https://p.dw.com/p/16DMi
Iranian President Mahmoud Ahmadinejad speaks at the conclusion of an annual pro-Palestinian rally, marking Quds (Jerusalem) Day, on the last Friday of the holy month of Ramadan, at the Tehran University campus, in Tehran, Iran, Friday, Aug. 17, 2012. Iran's president says Israel's existence is an "insult to all humanity." It's one of his sharpest attacks yet against the Jewish state. It comes as Israel openly debates whether to attack Iran over its nuclear program. Iran and Israel have been bitter enemies for decades. Israel considers Iran an existential threat because of its nuclear and missile programs and repeated references by Iranian leaders to Israel's destruction. (Foto:Vahid Salemi/AP/dapd).
Mahmud Ahmadinedschad Präsident IranHoto: AP

Har wa yau mahukuntan na Tehran sun ce ƙasar za ta ƙauracewa bikin bada kyauta na Oscars ga wanda su ka yi bajinta wajen shirye fina-fianai a shekara mai zuwa muddin masu shirya gasar ba su yi Allah wadai da fim ɗin nan da ya ci zarafin Musulunci ba.

Da ya ke jawabi ga kamafanin dillancin labarai na Mehr, wani mai magana da yawun gwamnatin ta Iran ya ce ɗaukar wannan matakin ya zama dole bayan da galibin al'ummar ƙasar su ka buƙaci Tehran ɗin ta yi hakan.

A tasa zantawar da manema labarai ministan da ke kula da harkokin al'adu na ƙasar Javad Shamgadri cewa ya yi mahukuntan ƙasar ba su da wani zaɓi da ya wuce rungumar buƙatun jama'arsu kuma dole ne su nuna fushinsu kasancewa an yi karen tsaye ga addininsu da ke da mabiya kimanin biliyan ɗaya da rabi a faɗin duniya.

Mawallafi : Ahmed Salisu
Edita : Saleh Umar Saleh