1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An rataye mai adawa da gwamnatin Iran

Ramatu Garba Baba
December 12, 2022

Iran ta kuma aiwatar da hukuncin kisa ta hanyar rataya kan wani dan kasar da ta zarga da hannu a mutuwar wasu jami'an tsaro a yayin wata zanga-zanga a watan Nuwamba.

https://p.dw.com/p/4KoAM
Majid Reza, mutum na biyu da Iran ta rataye saboda zanga-zanga
Majid Reza Rahnavard, mutum na biyu da Iran ta rataye saboda zanga-zangaHoto: UGC

Mahukuntan kasar Iran sun sake aiwatar da hukuncin kisa kan daya daga cikin masu zanga-zangar kin jinin gwamnatin kasar da ya jima a tsare.

An aiwatar da hukuncin kisan kan Majidreza Rahnavard ne bayan da kotu ta same shi da laifin hannu a kisan wasu jami'ai biyu na rundunar nan ta Basij da ta yi kaurin suna wajen amfani da karfi yayin kwantar da tarzoma a kasar.

A makon da ya gabata ma dai, mahukuntan na Tehran sun bayar da umarnin rataye wani mai zanga-zanga Mohsen Shekari bisa laifin jikkata wani jami'in tsaro a yayin zanga-zangar.

Yazuwa yanzu, an kiyasta cewa masu zanga-zanga sama da dubu goma sha biyar aka kama, inda aka gurfanar da mutum dubu biyu tare da yanke musu hukuncin kisa a hukumance.

Iran ta fada cikin rudani, tun bayan mutuwar matashiya Mahsa Amini da ake zargin ta mutu saboda azabar da jami'an Hisbah suka gallaza mata bisa laifin kin mutunta dokar sanya hijabi.