1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iran ta haramta wa kanta kera makamin kare dangi

July 20, 2022

Karo na biyu cikin watanni 18 ke nan da Iran ta fito ta wanke kanta daga zargin sarrafa makamai masu guba. Kalaman na zuwa ne a yayin da ake ci gaba da tattaunawa mai zafi a tsakanin Iran da Kasashen Yamma a kan batun.

https://p.dw.com/p/4EPTK
Russland Moskau, Besuch Iran Ebrahim Raisi
Hoto: Pavel Bednyakov/Kremlin/Zuma/picture alliance

Hukumomi a Iran sun ce har yanzu ba su sauya manufarsu kan kera makaman nukiliya ba. Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Iran, Nasser Kanani, ne ya shaida wa 'yan jarida hakan a wannan Laraba, inda ya ce  mahukunta a Tehran na da fatwa da ta haramta kera makaman kare dangi. 

Wannan bayani dai ya biyo bayan wata hira da gidan talabijin na Aljazeera ya yi da wani babban jami'in gwamnatin kasar, wanda ya ce Iran na da kayan aikin da za ta iya sarrafa makaman kare dangi.