1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iran ta kakaba wa 'yan Turai takunkumi

Mouhamadou Awal Balarabe
October 26, 2022

Iran ta sanar da kakaba takunkumi kan cibiyoyi da daidaikun mutane da kafafen yada labarai da ke kasashen kungiyar Tarayyar Turai, a matsayin martani ga matakan ladabtarwa da EU ta dauka kan masu murkushe zanga-zanga.

https://p.dw.com/p/4IhwY
Gipfel der Shanghaier Organisation für Zusammenarbeit in Duschanbe - Tadschikistan | Ebrahim Raissi Präsident Iran
Hoto: SalamPix/ABACA/picture alliance

Wasu 'yan majalisar dokokin Faransa da kuma manaima labarai biyu na jaridar Bild ta Jamus na daga cikin wadanda gwamnatin Iran ta sanya wa takunkumi. A cikin sanarwar da ta fitar a birnin Teheran, ma'aikatar harkokin wajen Iran ta zarge su da goyon bayan 'yan ta'adda tare da haddasa tashin hankali a kasar.

Takunkumin ya hada da haramta musu biza da kuma kwace dukiyoyi da kadarorinsu a yankin da ke karkashin ikon Iran. Wannan mataki ya zo ne mako guda bayan da Iran ta fara sanya takunkumi kan wasu jami'ai da hukumomin Birtaniya, bayan da Landan ta kakaba wa 'yan sandan da'a na Iran takunkumi saboda mutuwar Mahsa Amini.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da dubban mutane suka taru a kabarin matashiya Mahsa Amini a yankin Kurdistan domin yi mata adu'o'i na karshen makokin kwanaki 40 da aka saba a Iran.