1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

IAEA: Iran ta kara yawan uranium dinta

Lateefa Mustapha Ja'afar
July 8, 2019

Hukumar Kula da Makamashin Nukiliya ta Kasa da Kasa IAEA, ta tabbatar da cewa kasar Iran ta inganta makamashinta na uranium fiye da yadda yarjejeniyar nukiliya ta amince mata na sama da kaso uku a shekara ta 2015.

https://p.dw.com/p/3Llkc
Die iranische Flagge vor der Zentrale der Internationalen Atomenergie-Organisation (IAEO) in Wien
Iran ta yi fatali da yarjejeniyar nukiliya ta 2015Hoto: Reuters/L. Foeger

Darakta janar na hukumar Yukiya Amano ya shaidawa mambobin gudanarwa na hukumar cewa kawo yanzu Iran ta kara yawan makamashin nata zuwa sama da kaso hudu, kamar yadda ta shelanta a karshen mako da kanta. Rahoton ya kara da cewa sai dai har yanzu makamshin nata bai kai adadin kaso 20 da take sarrafawa gabanin yarjejeniyar ta 2015 ba kuma ba zai isheta ta sarrafa makaman kare dangi ba. Matakin na Iran dai na zuwa ne bayan da Amirka ta fice daga cikin yarjejeniyar nukiliyar ta 2015 tare kuma da kakabawa Tehran sababbin takunkuman karya tattalin arziki, inda Iran din ta bukaci kasashen Turai da su yi wani abu da zai taimaki tattalin arzikinta da ya tsunduma cikin rudani amma hakan ta gagara. A hannu guda kuma mataimakin shugaban kasar Amirkan Mike Pence ya sanar da cewa za su ci gaba da matsawa tattalin arzikin Iran din lamba tare kuma da shan alwashin kare muradun Amirkan a yankin Gabas ta Tsakiya.