1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Cire kamarori a tashoshin makamashinta

Binta Aliyu Zurmi
June 8, 2022

Rahotanni daga Iran na nuni da cewar an cire kamarori da ke samar wa hukumar kula da makamashin nukilya bayanai a kan al'amuran da ke faruwa a wasu tashoshin da Iran ke samar da makamashinta.

https://p.dw.com/p/4CQdb
Iran Atomenergie Flash-Galerie
Hoto: picture alliance/dpa

Wannan mataki dai ka iya kara dagula al'amura tsakanin Iran din da hukumar ta Majalisar Dinkin Duniya da ke saka idanu a kan makamashin.

A cewar mai magana da yawun hukumar da ke samar da makamashin nukiliyar Iran din Behrouz Kamalvandi, ba za su lamunci yadda hukumar ke wuce gona da iri ba, ya kuma kara da cewar yana fatan za su gane illar abin da suke yi su kuma ba wai Iran din hadin kan da ya kamata.

Ko a watan da ya gabata dai Iran ta ki bude wa hukumar kula da makamashin nukiliya kofa domin ganin yawan sinadarin Uranium da ta mallaka, lamarin da ya sanya hukumar zargin Iran da mallakar abin da ya wuce kima.

Kasashen Amirka da Birtaniya da Jamus gami da Faransa sun fusatar da Iran da suka ce ba ta mutunta yarjejeniyar da aka cimma.