1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iran ta aiwatar da hukuncin kisa kan masu zanga-zanga biyu

Binta Aliyu Zurmi
January 7, 2023

Iran ta zartas da hukuncin kisa kan wasu masu zanga-zanga biyu a wannan Asabar, hukuncin ya biyo bayan samunsu da ta ce ta yi da laifin kashe wani jamiIn tsaro a lokacin zanga-zangar adawa da mutuwar Mahsa Amini.

https://p.dw.com/p/4LrKT
Deutschland l Iran Protest l Solidarität und Protest gegen das Iranische Regime in Köln
Hoto: Uwe Geisler/Geisler-Fotopress/picture alliance

Wadanda aka kashen sun hada da Mohammed Mahdi Karami da Seyyed Mohammad Hosseini. Tun dai bayan barkewar zanga-zangar adawa kan mutuwar Mahsa Amini a watan Satumbar bara, an yankewa mutum fiye da hudu hukuncin kisa ta hanyar rataya a kasar ta Iran, lamarin da ya janyo wa kasar suka daga manyan kasashen duniya.

Ko a nan birnin Bonn da yammacin yau daruruwan al'umma ne suka gudanar da zanga-zangar yin Allah wadai da matakin da mahukuntan na Iran ke dauka a kan masu boren. 

A cewar dan majalisar dokokin Jamus Helge Limburg, Jamus da Amirka gami da kungiyar tarayyar Turai ba za su zuba ido a kan hukuncin kisa da mahukuntan Tehran ke aiwatarwa a kan fararen hula ba.