1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iraki ta mikawa Turkiyya yaran IS 200

Abdul-raheem Hassan
May 29, 2019

An dai mika yaran ne a birnin Bagadaza a gaban wakilan ma'aikatar harkokin wajen Iraki da Turkiyya da sauran wakilan kungiyoyin kasa da kasa ciki har da asusun kula da kananan yara ta MDD UNICEF.

https://p.dw.com/p/3JS2i
IS Kinder
Hoto: NDR

Wata kotu a Iraki ta tabbatar da mika yaran da IS suka bari a kasar kusan 200 ga hukumomin kasar Turkiyya bayan ayyana murkushe mayakan IS a watan Disamban 2017. Kungiyar IS ta shafe kusan shekaru uku suna rike da iko a wasu yankunan arewacin Iraki, amma duk da ikirarin gwamnati suna kai harin sari ka noke da yin garkuwa da mutane a sassa dabam-dabam.