1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iraƙi ta ce ba a kaiwa Siriya makamai ta ƙasarta

September 20, 2012

Mahukuntan Iraƙi sun musanta zargin cewa Iran na amfani da sararin samaniyana wajen kaiwa gwamnatin Siriya makamai a yaƙin da ta ke da 'yan ta'adda.

https://p.dw.com/p/16BxN
A Free Syrian Army fighter is pictured holding a rocket-propelled grenade (RPG) under Al-Sakhur bridge in Aleppo September 18, 2012. REUTERS/Zain Karam (SYRIA - Tags: CONFLICT CIVIL UNREST POLITICS)
Hoto: Reuters

A jiya Laraba ce dai kamafanin dillancin labarai na Reuters ya rawaito wannan labarin inda ya ƙara da cewar sojojin ƙundunbala na Islamic Revolutionary Guard ne kan gaba wajen kai makaman ga Siriya ta hanyar amfani da jirage da kuma motocin yaƙi.

Da ya ke maida martani kan wannan zargin, mai magana da yawun gwamnatin ta Iraƙi Ali al-Dabbagh ya shaidawa manema labari cewar tuni gwamnatinsu ta sha alwashin kin tallafawa Siriya ko kuma sanya hannu wajen kaiwa Siriyan makamai ko dai ta sararin samaniyanta ko kuma ta ƙasa.

Mr. al-Dabbagh ya ƙara da cewar ƙasarsu a ko da yaushe shirye ta ke wajen bada gudumawarta wajen katse kaiwa gwamnatin Siriya makamai a yaƙin da ta ke da yi da masu rajin kawo sauyi.

Mawallafi : Ahmed Salisu
Edita : Umaru Aliyu