1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Inganta tsaro a Nijar da Mali da Burkina Faso

Gazali Abdou Tasawa AH
March 15, 2022

Kokarin fahimtar da juna tsakanin jam'ian tsaro da kuma kungiyoyin agaji masu gudanar da ayyukan jin kai a yankunan da ake fama da matsalar tsaro na magangamar iyakokin kasashen Nijar da Mali da Burkina Faso.

https://p.dw.com/p/48W2G
Schwere Schusswechsel in mehreren Kasernen in Burkina Faso
Hoto: Sophie Garcia/AP/dpa/picture alliance

Wasu alkalumman Majalisar Dinkin Duniya sun nunar da cewa miliyoyin jama’a ne matsalar tsaro mai nasaba da ayyukan kungiyoyin 'yan ta’adda da ake fama da ita a yankin magangamar iyakokin kasashe uku na Nijar da Mali da Burkina Faso suke cikin tsananin bukatar agji. To amma kuma rashin samun fahimtar juna tsakanin jami’an tsaro da kungiyoyin agaji na ciki da ma na wajen kasar masu aiki a yankunan na kawo cikas ga kokarin da ake tallafa wa mutanen. Domin shawo kann wannan matsala ce hukumar kula da ayyukan jin kai ta MDD wato OCHA da kuma hukumar kula da hakkin dan Adam ta MDD ne suka shirya wani taro da nufin samar da fahimtar juna tsakanin bangarorin biyu. Assoumana Abdourahmane na Hukumar koli mai kula da karfafa zaman lafiya a Nijar wato HACP daya daga cikin mahalarta taron ya yi karin bayani kan ma’anarsa: '' Idan muka bukaci rakkiyar jami’an tsaro hadarin da ke da akwai shi ne kasancewa kungiyoyin 'yan ta’adda na yaki kai tsaye da jami’an tsaro, to sukan iya farmamu tare, idan kuma muka tafi babu rakkiyar jami’an tsaro hadarin da ke da akwai shi ne ‚yan ta’addan na tare jami’an agajin su kwace mausu motoci da sauran kayan aiki da ma yin garkuwa da mutane musamman idan 'yan kasashen waje ne. Don haka muna fatan a wajen wannan taro za mu samu amsa ta sanin wani loakci ne ya kamata mu samu rakkiyar jami’an tsaro, wani loakci ne kuma bai dace ba“.