Inganta huldar Amirka da Afirka
July 28, 2015
Jawabin dai shi ne irin sa na farko da shugaban kasar ta Amirka ya yi wa mambobin kasashen AU, wanda hakan ke nuni da cewar Amirka da kasashen Afrikan na kokarin karfafa dangantaka da juna.
Obama yace: "Burin mu shi ne mu kara bunkasa harkokin ayyukan noma ga kananan manoma a daukacin nahiyar Afrika. Abin da muka sani shi ne mafi yawancin yan Afrika na samun kudin shiga ne ta hanyar ayyukan gona, kuma mafi yawancin gonakansu kanana ne, kana kuma babu wata alamar bunkasar fasaha, to amma idan aka tallafa musu za su sami gagarumin ci-gaba.
Tun da farkon dai sai da shugaba Obaman ya kara tunatar da duniya cewar nahiyar Afrika, na daya daga cikin nahiyoyin da tattalin arzikinsu ke ci-gaba da habaka a duniya.
Kazalika shugaba Obaman ya yi amfani da zauran taro a inda ya kara jan kunnen shugabanin Afrika wajen mutunta wa'adin shugabanci, tare da nuna halin dattaku wajen bin doka da oda gami da kawo karshen cutar ciwon daji da kuma cin hanci da rashawa.
A yayin da Obaman yake jawabin a gaban zauran taron ya jaddada cewar, nahiyar Afirka ta nunawa duniya misali a kan abubuwa da dama, yace:
"Dole ne mu yi riko da halin mutuntaka da dan adam ya gada, muhimin abin shine ta yin la'akari da kusantar junanmu ko da daga ina kazo ko ka fito ko kuma yadda muke, duk kaninmu hallita daya ce. Kowa yana da bukatar wani abu a wajen wani, kuma ko wane mutum yana bukatar a girmama shi a bisa mutuntaka"
Babban kudirin ziyarar ta Obama a Afrika shine, yadda Amirka za ta kara dankon zumunci da nahiyar, kana ta tallafa wa nahiyar wajen kara habaka harkokin tattalin arziki, tare da janyo hankulan jagororin kasashen na Afirka a kan batutuwan da suka shafi dakile cin hanci da rashawa, kare hakkokin Bil Adama, mutunta aiyukan 'yan jaridu da kuma jan damara wajen samar da guraben ayyukan yi ga dubban matasan a nahiyar Afirka.
Ita ma a bangaren shugabar hukumar gudanarwar kungiyar AU Dlamini Zuma, ta bukaci shugaba Obama da ya sake waiwayar kuskuren da aka tafka, a dangane da batun nema wa nahiyar Afirka kujerar dindin-din a zauran Majalisar Dinkin Duniya, a inda ta ce rashin hakan rashin adalci ne babba ga nahiyar baki daya.