Inganta cinikayya tsakanin Jamus da China
May 27, 2013Kamfanoni a nan Jamus sun bi sahun shugabar gwamnatin kasar, Angela Merkel wajen neman a cimma yarjejeniyar sulhu domin kawo karshen barazanar samun yakin kasuwanci tsakanin nahiyar Turai da kasar Sin wato China.
Shugaban kwamitin Asia-Pacific da kungiyar kampanonin Jamus ta samar, domin wakiltar bukatun yankin Asiya Peter Loesche yace, duba da yadda ake kara samun matsala tsakanin Tarayyar Turai da kuma kasar China, suna bukatar da a tatauna domin samun sulhu a tsakani.
Wannan bayani na Loescher na zuwa ne gabanin taron da za a gudanar tsakanin shugabannin 'yan kasuwar Jamus da China a birnin Berlin, tare da shugaban Kasar China Li Keqang da a yanzu haka yake ziyarar aiki a nan Jamus.
Mawallafiya: Lateefa Mustapha Jaafar
Edita: Mohammad Nasiru Awal