1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaIndonesiya

An bude runfunan zaben a Indonesiya

Abdourahamane Hassane
February 14, 2024

Kimanin mutane miliyan 205 ake sa ran za su kkada kkuri'a a zaben shugaban kasa da na 'yan majalisun dokoki.

https://p.dw.com/p/4cNJ7
Shugaba mai barin gado Joko Widodo
Shugaba mai barin gado Joko WidodoHoto: Mas Agung Wilis/AFP/Getty Images

Al'umma ta fara  kada kuria a zaben shugaban kasa da na 'yan majalisar dokoki a Indonesiya,inda ake sa ran kimanin mutane miliyan 205 za su kada kurii'a. 'Yan takara guda uku ne dai za su fafata a zaben a ciki har da ministan tsaro na yanzu Prabowo Subianto,tsohon janar na soji. Ko da yake ana zarginsa da take hakkin dan Adam a karkashin mulkin kama-karya na Suharto a karshen shekarun 1990, Amma dai ana  ganin tsohon janar din mai shekaru 72 na iya yin nasara a zagayen farko na zaben domin ya gaji Joko Widodo wanda ya kammala wa'adinsa biyu.