1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Indiya ta kori 'yan gudun hijirar Rohingya

Ramatu Garba Baba
October 5, 2018

Gwamnatin kasar Indiya ta meka wasu 'yan Rohingya bakwai a hannun hukumomin kasar Myanmar bayan da kotu ta yi facali da bukatarsu ta neman mafaka daga rikicin kabilanci.

https://p.dw.com/p/3610E
Indien Rohingya-Flüchtling beobachtet Myanmars Tragödie bei WhatsApp
Hoto: DW/Ashish Malhotra

Mutanen bakwai na daga cikin dubban 'yan kabilar Rohingya da suka tserewa rikicin kabilanci suka kuma nemi mafaka a Indiya, hukumomin Indiyan sun kin amincewa da bukatarsu ta neman mafaka duk da barazanar rasa rayukansu da suka ce za su fuskanta muddun aka tilasta musu komawa gida.

Kungiyar kare hakkin dan Adam ta Amnesty International ta soki wannan mataki, inda ta ce bai kamata a yi facali da barazanar da rayuwar wadannan mutanen ke ciki in har sun koma gida ba. An dai dauki matakin ne bayan da kotun  da aka shigar da koken mutanen gabanta ta yi fatali da bukatar ba su mafaka, akwai zargin da ake wa wasu daga cikin dubban 'yan gudun hijirar da ke samun mafaka da ra'ayi irin na masu tsatsauran ra'ayin addini da Indiyan ke ganin barazana ce ga tsaron kasa.