1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAsiya

Jagoran Indiya ya taya firamnistan Pakistan murna

Suleiman Babayo ZUD
March 5, 2024

A wani matakin da ba a saba gani ba, Firaminista Narendra Modi na Indiya ya taya takwaransa sabon Firaminista Shehbaz Sharif na kasar Pakistan murnar sake dawowa kan madafun iko.

https://p.dw.com/p/4dCFF
Pakistan, Islamabad | Sabon Firaminista Shehbaz Sharif na Pakistan
Sabon Firaminista Shehbaz Sharif na PakistanHoto: Pakistan's President Office/AP/picture alliance

Firaminista Narendra Modi na kasar Indiya ya taya takwaransa sabon Firaminista Shehbaz Sharif na kasar Pakistan murnar sake dawowa kan madafun iko, a wani abin na ba kasafai ba, saboda tsamin dangantaka tsakanin kasashen biyu masu makwabtaka da juna kuma duk suke da karfin makamun nukiliya.

A wannan Litinin da ta gabata aka rantsar da sabon Firamnista Sharif na kasar ta Pakistan bayan zabe mai cike da rudanin zargin magudi da ya gudana a kasar.

Kasashen Indiya da Pakistan sun shafe shekara da shekaru suna rkicin kan iyaka tun bayan samun 'yanci daga Turawan mulkin mallaka na Birtaniya da aka raba kasar ta Indiya gida biyu aka kirkiro Pakistan.