1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Indiya ta Kaddamar da rigakafin corona

Abdoulaye Mamane Amadou
January 16, 2021

Mutune miliyan 300 ne ake sa ran yi wa allurar rigakafin kamuwa da coronavirus kafin watan Yuli a Indiya, bayan da aka kaddamar da gangamin farko na alluran rigakafin yaki da cutar Covid-19.

https://p.dw.com/p/3o0P8
COVID-19-Impfung in Indien
Hoto: David Talukdar/NurPhoto/picture alliance

Kasar Indiya mai yawan al'umma biliyan 1,3 ta soma gudanar da allurar rigakafin Corona a daidai lokacin da kasar ke fama da matsalar yawan yaduwar cutar, kana kasar ko baya ga jami'an lafiya, ta ware karin mutane 150.000 da za su taimaki malaman kiwon lafiya wajen zartar da aikin rigakafin a wasu cibiyoyin allurai 700 da kasar ta tanada.

Sai dai bisa matsalolin sufurin allura daga wasu yankunan zuwa wasu, za a soma  yi wa jami'an kiwon lafiya da wadanda suke tattare da hadarin kamuwa da cutar corona allurar a matakin farko, inda ake hasashen za su haura akalla mutun miliyan 30.