1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Indiya na samun taimakon kasashen duniya

April 27, 2021

Kasashen duniya sun tashi wajen ganin sun tallafa wa Indiya, sakamakon yadda take asarar rayukan 'ya'yanta da corona ke halakawa. Kasar ce ta fi yawan mutuwar daga coronar.

https://p.dw.com/p/3sdOq
Indien | Coronavirus | Hilfsflug mit medizinischen Gütern aus Großbritannien erreicht Flughafen Neu Delhi
Hoto: ANI/REUTERS TV

Rukunin farko na tallafin kayayyakin lafiya sun isa kasar Indiya a wannan Talata, yayin da kasar ke fama da ta'adin annobar corona wanda ke ci gaba da janyo hasarar rayukan mutane masu yawa a kulli yaumin, fiye da kowace kasar duniya a halin yanzu.

Cutar ta corona dai na ci gaba da barna a kasar ta Indiya, inda wadanda take kamawa ke fin karfin asibitoci da sauran kayayyakin aiki da ake bukata domin ceto rayuwar majinyata, daidai kuma lokacin da wasu kasashen duniya ke shirin sassauta matakan yaki da cutar.

Kasar Amirka ta yi alkawarin kai wa kasar ta Indiya daukin miliyoyin alluran rigakafin AstraZenica domin fara aiki da su wajen bai wa wasu daga cikin 'yan kasar kariya.

Sama da mutum dubu biyu da 800 ne dai cutar ta kashe a jiya kadai a Indiyar, yayin kuma da wadanda suka matu a jiyan kadai suka zarta mutum dubu 320.