1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mutane 5 sun mutu a Indiya sakamakon gobara

Zulaiha Abubakar
May 7, 2020

Kimanin mutane 5 sun mutu yayin da kusan 1000 ke kwance a sibiti sakamakon tashin gobara a wata ma'ajiyar sinadarai a jihar Andhra Pradesh da ke a Gabashin Indiya a wannan Alhamis din.

https://p.dw.com/p/3bsUu
Indien Chemieunfall bei Visakhapatnam
Hoto: AFP

Jami'an kashe gobara sun baiyana cewar gobarar ta tashi ne sakamakon fitar iskar gas ta wani bututu da ya fashe a wannan lokaci da ake zaman gida. Sai dai hukumar kashe gobarar ta tsoratar game da samun iyalai cikin mawuyacin hali a cikin gidajensu sakamakon shakar iskar gas.

Daga cikin mutanen da ke kwance a asibiti akwai mata da kananan yara, a nata bangaren hukumar yan sanda ta bayyana shirin bi gida-gida domin gano yanayin da makwabtan ma'aijar sinadaran ke ciki.