1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Indiya: Mahaukaciyar guguwa ta kashe mutane

Ahmed Salisu
May 21, 2020

Wata mahaukaciyar guguwa da ta fadawa kasar Indiya ta yi sanadin rasuwar mutum saba'in da biyu kana ta haddasa katsewar wutar lantarki da lalata gidajen mutane a dama.

https://p.dw.com/p/3caQM
Indien Zyklon Amphan
Hoto: Reuters/R. de Chowdhuri

Guguwar wadda aka yi wa lakabi da Amphan ta afkawa gabashin kasar ta Indiya ne musamman ma dai jihar nan ta West Bengal kuma ta fara wannan ta'adi nata ne tun daga jiya Laraba.

Baya ga gabashin Indiya da wannan ibtila'i ya shafa, rahotanni na cewar lamarin ya shafi kasar Bangladesh wadda ke makotaka da kasar ta Indiya inda nan ma guguwar ta yi ta'adi har ma aka bada labarin rasuwar mutum akalla goma.