1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Masu jinyar corona 13 sun mutu a gobara

Binta Aliyu Zurmi
April 23, 2021

Wata gobara da ta tashi a asibitin Vijay Vallabh da ke wajen birnin Mumbai na kasar Indiya ta yi sanadiyar mutuwar majinyata masu dauke da cutar coronavirus su goma sha uku.

https://p.dw.com/p/3sSId
Indien Greater Noida | Sharda Hospital
Hoto: Getty Images/AFP/X. Galiana

An yi nasarar kashe gobarar kuma tuni aka fara binciken musababin tashin wutar.

Gobarar dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da kasar ke fama da karuwar sabbin masu kamuwa da cutar a karo na biyu, da ma sabon nau'in cutar da kasar ke fama da shi a yanzu haka.

Karancin iskar Oxygen da ake sanyawa marasa lafiya na daga cikin manyan matsalolin da fannin kiwon lafiya na kasar ke fuskanta. 

Tuni mahukunta suka haramta duk wani taro na addini da ma na siyasa tare da saka tsauraran matakan kulle da zai ba su damar shawo kan wannan annoba da ke ci kamar wutar daji.