1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

IMF: Zambiya za ta amso bashi daga ketare

October 12, 2023

Babbar daraktar asusun bada lamuni na duniya IMF, Kristalina Georgieva ta ce kasar Zambiya ta sanya hannu kan yarjejeniyar karbar bashi daga kasashen ketare.

https://p.dw.com/p/4XTNB
Taron Asusun bada lamuni na duniya, IMF a birnin Marrakesh na kasar Moroco
Taron Asusun bada lamuni na duniya, IMF a birnin Marrakesh na kasar MorocoHoto: Abu Adem Muhammed/AA/picture alliance

Hakan dai zai bai wa kasar da ke zama ta farko a nahiyar Afirka da ta kasa biyan basukanta bayan annobar corona damar samun tallafin kudi.

Zambiyar dai ta cimma yarjejeniyar ce da masu bata rance da suka hada da China da kuma kasashen yammacin Turai yayin taron asusun na shekar-shekara da ke gudana a birnin Marraksesh na kasar Moroco. 

Karin bayani:Zambiya: Mafita kan bashin IMF da China 

Ministan kudin Zambiya, Situmbeko Musokotwane ya ce koda yake kudin ba zai samarwa matasan Afirka irin rayuwar da suke so ba, sai dai zai taimaka wajen samar da guraben aiki wanda ka iya hana matasan salwantar da rayuwarsu a tekun Bahar rum a yunkurin tsallakawa kasashen Turai domin neman rayuwa mai inganci.