1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Tattalin arzikiGhana

Ghana za ta samu bashi daga IMF

October 6, 2023

Kasar Ghana ta cimma yarjejeniya da Asusun ba da Lamuni na Duniya IMF ta bashin dalar Amurka biliyan uku, inda za a fara ba ta dala miliyan 600.

https://p.dw.com/p/4XDUj
Ghana | Nana Akufo-Addo
Shugaban kasar Ghana Nana Akufo-AddoHoto: Anthony Anex/KEYSTONE/picture alliance

Kafin alkalmin na dala miliyan 600 da Ghanar za ta karba, zaai samu ne da zarar hukumar gudanarwar asusun na IMF ta sahale. Wata sanarwa da asusun ya fitar, ta ce wajibi ne Ghana ta hanzarta kammala nazarin tsarin da za ta bi wajen biyan bashin da kuma yadda za ta kashe kudin kamar yadda suka fara tattaunawa a kai a cikin watan Mayun wannan shekara. A bara ne dai Ghana ta nemi agajin asusun na IMF don ceto ta daga matsanancin halin matsin tattalin arzikin da ta shiga, wanda ke zaman mafi muni cikin tsawon shekaru.