illar ma'adinai a kasar Kwango:
Ma'adinan Cobalt da coltan na nan barjak a Jamhuriyar Demukaradiyyar Kwango. Amma rashin tsaron yankin ya dagula komai, ma'adinan suna jawo hankalin mayaka, inda suke haddasa cin zarafi da tashin hankali.
Tattalin arziki da kuma sanadin tashin hankali
A lardin gabashin Jamhuriyar Demukaradiyyar Kwango da ake fama da rikici, arziki kamar zinare da bakin karfe, na jawo hankalin mayaka da ke amfani da damar hakan inda suke tada hankalin jama'a, ciki har da yara kanana wadanda ake tilasta wa hakar ma'adinai don samun kudin sayan makamai, inda za'a samu damar mallakar karin filaye ta yadda yakin zai dore.
Kare 'yan kasa da tabbatar ana hakar ma'adinai bisa doka
MONUSCO, da ke zama rundunar MDD mafi tsadar ayyukan zaman lafiya, na kokarin samar da zaman lafiya a Arewaci da Gabashin Kivu, wacce ke zama tsakiyar tashin hankalin kasar. Jami'an tsaro na sintiri a kauyen Nzibira mai wuraren hakar ma'adinai da ke iyaka da Zola Zola, wurin da ake hakar ma'adinai bisa doka.
Ci da gumin talaka wajen hada wayar salula
Cassiterite ma'adini ne da ke hada sinadarin wayar salula. Rabin wayoyin salulan duniya, sinadarin hadasu na fituwa ne daga tsakiyar Afirka. A Jamhuriyar Demukaradiyar Kwango ma'adinai sun kasance karkashin kulawar jami'an tsaron tun a shekara ta 2010, a lokacin da Amirka ta sa dokar cewa dukkan kamfanin da ke sayan ma'adinai dole su kasance ba daga yankuna da ke fama da tashin hankali ba ne.
Tabbatar da ma'adinai na halal
Wani allo a Nzibira da ke nuna yadda ake son buhunan ma'adinai su kasance, ta haka ne kamfanonin Amirka za su san an hako ma'adinan ne bisa doka. Amma tsarin na da rauni mai yawa. Bata-gari kan hako ma'adinai a haramtacciyar hanya su bi bayan gida su sayar wa wadanda ke da lasisin halal, a zuba cikin buhuna da ke da alamar an bi doka.
Ci da gumin yara
Duk da kokarin kungiyoyin kare hakki jama'a, cin zarafi ya zama ruwan dare a wuraren hakar ma'adinan a Jamhuriyar Demukaradiyyar Kwango. Yara kamar Esperance Furahaare, wacce aka saceta, mayaka suka yi mata fyade a lokacin ta na 'yar shekaru 14. wannan ya zama ruwan dare ga cin zarafi da azabtarwa.
Illar gurbataccen muhalli
Hakar ma'adinai da ke da yuwar sa-idon hukuma, zai iya zama illa ga muhalli da jama'ar da ke zama kusa da shi. A wuraren haramtattun hakar ma'adinai, dagwalo na iya kwarara cikin ruwan shan jama'a ya gurbatashi.
Rashin tabbas ga makomar dokokin magance ma'adinai da ke jawo tashin hankali
'Yan majalisar dokokin Amirka na kokarin samar da kudurin da zai kawar da dokar 2010. Wakilai na aza tambaya kan dokar ko ba ta duba cin zarafi a kasashen tsakiyar Afirka, a daidai lokacin da kamfanonin ke tabbatar ma'adinan da suke sayowa ba na haram ba ne, abin da ake bukata garesu shi ne su tambayi masu sayarwa, bawai su tantance kayan da suke saya ko asalin inda ya fito ba.