1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ikrarin lashe zaben Tunusiya

Gazali Abdou Tasawa
September 16, 2019

Wasu 'yan takara biyu na a Tunusiya, sun yi ikirarin kasancewa sahun gaba a sakamakon zaben shugaban kasa da aka gudanar a karshen mako tsakanin 'yan takara 26.

https://p.dw.com/p/3Peb2
Kommunalwahlen in Tunesien
Hoto: picture-alliance/AA/Y. Gaidi

'Yan takarar biyu na wato Nabil Karoui hamshakin attajirin nan da ke tsare a gidan kaso bisa zargin tsarkake kudaden haram da kuma Kais Saied dan takara mai zaman kansa, sune suka yi ikrarin kasancewa a sahun gaban, a zaben shugaban kasar da ya gudana a karshen mako.

Wasu cibiyoyin kididdigar sakamakon zabe masu zaman kansu, sun bayyana cewa Kais Saied na a kan gaba da kaso 19 daga cikin dari a yayin da Nabil Karoui ya samu kaso 15 daga cikin 100 na kuri'un da aka kada, wanda ke nufin cewa sune za su fafata a zagaye na biyu na zaben shugaban kasar.

 Idan dai har hukumar zaben kasar ta ISIE ta tabbatar da wadannan alkalumma a hakumance a gobe Talata, to kuwa hakan zai zamo wani babban ruguntsumi a fagen siyasar kasar ta Tunusiya, kasancewar babu daya daga cikin shugabannin siyasar kasar na bayan juyin-juya hali na 2011, da ya yi nasarar ketarawa zuwa zagaye na biyu na zaben wanda ya hada 'yan takara 26.