1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Siriya: 'Yan tawaye sun ki amincewa da sulhu

Zulaiha Abubakar
September 23, 2018

Wani bangare na 'yan tawaye a yankin Idlib da ke arewa maso yammacin kasar Siriya sun yi watsi da umarnin da kasashen Rasha da Turkiyya suka bada na cimma zaman lafiya.

https://p.dw.com/p/35Mfb
Türkei beginnt Offensive Operation Afrin in Syrien
Hoto: picture alliance/abaca/Depo Photos

Kasashen na Rasha da Turkiyya sun shawarci yan ta'addan da su kauracewa yankin da sojojin kasashen biyu suka yi sansani kafin ranar 10 ga watan Oktoba mai kamawa, a cigaba da yunkurin kawo karshen yakin kasar.

Da suke mayar da martani cikin wata sanarwa. 'yan tawayen sun umarci mayakan kungiyar da su cigaba da kai hare-hare. Akalla fararen hula miliyan uku ne ke zaune a yankin na Idlib kafin yakin da ake gwabzawa a kasar ya mayar da su 'yan gudun hijira.