1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An sami Dominic Ongwen da laifuffukan yaki

February 4, 2021

Kotun hukunta masu aikata manyan laififfuka ta ICC ta yankewa wani tsohon kwamandan 'yan tawayen Yuganda hukuncin daurin rai da rai.

https://p.dw.com/p/3osdT
Niederlande Dominic Ongwen vor dem  Internationalen Strafgerichtshof
Hoto: picture-alliance/AP Photo/P. Dejong

Kotun hukunta manyan laifuffuka ta duniya wato ICC ta sami tsohon kwamandan kungiyar yan tawaye ta Lord's Resistsnce Army da laifuffukan yaki da suka hada da kisa da fyade da kuma cin zarafin bil adama.

Kotun ta ICC ta yankewa Dominic Ongwen hukuncin daurin rai da rai, bayan da ta tuhume shi da laifuka guda sittin da daya.

Da fari dai an tursasawa Dominic Ongwen shiga kungiyar ta LRA tun yana dan yaro inda daga bisani ya zama daya daga cikin manyan kwamandojinta.

Daya daga cikin laifukan da aka sami kwamandan da hannu dumu-dumu a ciki shi ne wani hari da ya kai a wani sansanin 'yan gudun hijira inda suka hallaka mutane tare da yi wa mata fyade a farkon shekarun 2000.