1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

IAEA: Sinadarin 'uranium' na Iran abin tsoro ne

May 30, 2022

Hukumomin Iran sun ki bude wa hukumar kula da makamashin nukiliya kofa domin ganin yawan sinadarin 'uranium' da ta mallaka, lamarin da ya sanya hukumar zargin Iran da mallakar abin da ya wuce kima.

https://p.dw.com/p/4C3tn
IAEO-Generaldirektor Rafael Grossi
Hoto: Leonhard Foeger/REUTERS

Hukumar da ke kula da makashin nukiliya a duniya, IAEA, ta sanar a wannan Litinin cewa kasar Iran ta mallaki makamashin uranium da ya haura sau 18 na adadin da yarjejeniyar Iran da manyan kasashen duniya ta 2015 ta yi tanadi.


A cikin sabon rahoton da hukumar ta MDD ta fitar ta ce hukumomin Iran sun azurta kansu da sinadarin uranium da ya kai nauyin kilogiram kusan 4000 a maimakon kilogiram 300 da yarjejeniyar nukiliyar Iran din ta amincewa kasar.