1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Huldar cinikayya tsakanin Jamus da Indiya

December 12, 2010

Jamus da Indiya sun yi alkawarin bunkasa cinikayyar kasuwanci dake tsakaninsu

https://p.dw.com/p/QWIA
Firaministan Indiya Manmohan Singh da shugabar gwamnatin Jamus Angela MerkelHoto: picture alliance / dpa

Shugabannin kasashen Jamus da Indiya sun yi alkawarin rubanya harkokin cinikayya a tsakaninsu nan da shekaru biyu masu zuwa. Hakan ya biyo bayan tattaunawar da ta gudana ce tsakanin Firaministan Indiya Manmohan Singh da kuma shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel a birnin Berlin. Shugabar gwamnatin ta Jamus ta shaidawa yan jarida cewa kasashen biyu za su kara yawan cinikayyar zuwa sama da euro miliyan dubu Ashirin kafin karshen shekarar 2012. A nasa bangaren Firaministan Indiya Manmohan Singh ya yaba da kyakkyawar dangantakar dake tsakanin Indiya da Jamus. Shugabanin biyu sun yi ganawar ce a ranar Asabar din nan bayan taron da ya gudana tsakanin Indiya da kungiyar tarayyar Turai a Brussels inda suka cimma yarjejeniya ta fadada cinikayya ba tare da shamaki ba a tsakanin kungiyar tarayyar turan da Indiya. 

Mawallafi : Abdullahi Tanko Bala

   Edita  :    Umaru Aliyu