Hulɗa tsaro tsakanin Amirka da Masar
October 7, 2013Amirka na ware ko wacce shekara biliyan ɗaya da rabi ga ƙasar ta Masar domin tallafa wa harkokin soji da tsaro,kuma duk da ma sojojin sun kifar da zaɓaɓiyar gwamnatin Muhammed Mursi, amma har yanzu Amirka ba ta daina ba da tallafin ba saboda yadda ta ke kallon za ta rasa wani sukunmi na hannu a sha'anin tsaro a yanki da ke da mahimmanci a gareta.
Tushin yarjejeniyar ba da tallafin ga Masar da aka cimma
Ba da tallafin na soji ga ƙasar ya samo asili ne tun yarjejeniyar da Amirka ta ƙula da Masar ɗin a shekarun 1979.Kuma Masar ta kasance ƙasar da ke cike da mahimmanci ga Amirkar ba ma dan saboda mashigin teku ba na Canal de Suez , shi kansa batun tabbatar da tsaron Isra'ila na zaman wani abin da Amirkan ke karewa. To amma a yanzu shugaba Barack Obama ya ce za su saka ido a kan wannan batu.Ya ce : '' Abin da muke yi a yanzu na hulɗa tsakanin mu da Masar wani abu ne da ke tassar mana da tsada, amma babu shakku a kan wannan matsayi da aka cimma za mu duba abin da ya fi zama riba da alheri ga al'ummar Masar da kuma Amirka.''
Nazari na masu yin sharhi a kan wannan batu mai mahimmanci
Majalisun dokokin Amirka sun daɗe suna shakku a kan wannan shiri na tallafa wa sojojin, wanda da zaran sun amince da dokar ake isar da kuɗaɗen a cikin bankunan ga kamfanonin ƙera makamai da kayan yaƙi na soji wanda aka bai wa kamfanonin Amirka kwangilar ayyukan. Kuma kuɗaɗen da aka ware ba su fita daga Amirka domin abin kan kasance tuwo na mai na. Shana Marshall wata mai binciken kimiyya ce da ke a jami'ar George Washington wanda ta ce a kwai lauje cikin naɗi cikin wannan tallafi. Ta ce :''Lokaci zuwa lokaci a duk sanda maganar wannan tallafi ta zo a gaban 'yan majalisun dokoki, a kwai wasu manyan kamfanonin masu ƙera kayan yaƙi da tsaro, da ke tura mutanensu wajen 'yan majalisun dokokin domin yin kamun kafa. Cewar a kwai buƙatar a ci gaba da ba da tallafin sojin ga Masar saboda tsayawar shirin zai iya janyo rashin aikin yi ga wasu Amirkawan da kuma asara ga kamfanoni.''
Ba da tallafin ya dogara ga sauyi na demokradiyya da za a samu a Masar
Tun can da farko Obama ya yi gargaɗin cewar cire tallafin Amirka ga Masar ɗin ba zai dakatar da yunƙurin sojin da suka kifar da gwamnatin Mursi ba. Sannan kuma ba zai iya kawo wani sauyi ba, to amma dai ana ganin halin da ake ciki a ƙasar ya sa Amirkar cikin tsaka mai wuya inji Shana. Ta ce: '' Watakila waɗannan kuɗaɗen tallafi da ake bai wa Masar za a jirgitasu zuwa wasu ƙasashe inda Amirka ta ke da yarjeniya da su ta tsaro, irinsu Iraki da Afganistan da Pakistan da kuma Somaliya. Kuma kamfanonin Amirka da ke cin wannan gajiya shekara da shekaru na iya sake samin wannan kwangilar.
Daga ƙasa za a iya sararon wannan rahoto da kuma wanda wakilinmu na Masar ya aiko mana dangane da halin da ake ciki a Masar.
Mawallafi : Delcker Janosch/Hassane
Edita : Umaru Aliyu