1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hukuncin sake ƙidayar ƙuri'u a wasu mazaɓu a Kenya

March 25, 2013

Kotun koli a kasar Kenya ta yanke hukuncin sake ƙidayar ƙuri'un da aka kaɗa a zaɓen shugaban kasar a cikin mazaɓu 22 cikin dubu 32000 da ake da su.

https://p.dw.com/p/183tp
Auszählung der Wahlstimmen, Bhora Primary School im Stadtteil Westlands von Nairobi DW/ Maja Braun, Nairobi vom 4.3.2013
Hoto: DW/ M. Braun

Ɓangaran ɗan takara da ya sha kaye a zaɓen ne da aka gudanar a ƙasar ta Kenya a farkon wannan wata, wato Rail Odinga ya shigar da ƙara a gaban kotun kan cewar an yi aringizon ƙuri'u a wurare da dama. A zaɓen ɗai da aka gudanar a ranar huɗu ga watan Maris Uhuru Kenyyata ne ya samu rinjaye a gaban tsohon firaminista Rail Odinga, da kishi 50.7 cikin 100 na yawan ƙuri'un  da aka kaɗa shi kuma ya na da kashi 43 cikin 100. 

Kotun dai ta buƙaci dukkanin ɓangarorin biyu ko wane ya wakilta mutane goma da za su saka ido a sake ƙidayar ƙuri'un da za a yi kuma a kammala kafin nan da ƙarshen wannan mako.

Tun can da farko dai an yi ta samun fargaba na ɓarkewar tashin hankali a zaɓen. A shekarar 2007 a zaɓuɓbukan da aka gudaar a ƙasar mutane kusan dubu ne suka mutu sakamakon rigingimun da suka biyo bayan zaben.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita       :  Mohammad Nasiru Awal